Kano ta dauki lauyoyi 70 aiki domin inganta bangaren shari’a
Nigeria news
Gwamnatin Jihar Kano ta dauki lauyoyi 70 aiki.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a, Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Aliyu Yusuf, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa wannan shiri yana nufin inganta harkar shara’a tare da magance kalubalen rashin aikin yi a jihar.
“Shirin da gwamnan ya kirkiro ba shakka zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da ayyuka a bangaren shari’a na jihar, tare da magance matsalar rashin aikin yi,” inji Yusuf.
A cewar sanarwar, shugaban ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa, ne ya jagoranci gudanar da gwajin karshe na masu neman aiki, inda ya yabawa jagorancin hangen nesa na gwamnan.
Ya bayyana cewa wannan ci gaba zai karfafa bangaren shari’a na jihar, wanda tun da dadewa yake jiran irin wannan dauki.
Yayin da yake magana da sabbin lauyoyin da aka dauka, shugaban ma’aikatan ya shawarce su da su nuna gaskiya, jajircewa, sadaukarwa, da kuma kula wajen gudanar da ayyukansu.